2020-10-13 10:51:16 cri |
Guterres ya ce, bata gari suna kokarin hada kansu domin neman riba daga annobar COVID-19, ya kamata gwamnatoci su hada kansu don yin aiki tare karkashin tsarin yarjejeniyar MDD domin kawar da laifukan safarar bil adama, da fasa kaurin makamai, da sauran laifukan da ake aikata su wadanda suka ratsa cikin kasashe, jami'in MDD ya bayyana hakan ne a sakon bidiyo na taron kasashen duniya da suka sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa don yaki da muggan laifuka.
Taron na tsawon mako guda, wanda a hukumance shi ne karo na 10 na yarjejeniyar COP, ofishin MDD mai yaki da shan muggan kwayoyi da aikata laifuka ne ya shirya taron.
Kimanin kasashen duniya 190 ne suka amince da shiga yarjejeniyar, ita ce kadai yarjejeniyar da ta hada kasa da kasa domin tinkarar barazanar aikata muggan laifuka. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China