Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labarai na wajen Sin sun jinjinawa kwazon kasar a fannin shawo kan cutar COVID-19
2020-09-23 19:33:35        cri
A halin da ake ciki, matakan kandagarki da na shawo kan cutar COVID-19 da ake aiwatarwa a Sin, sun haifar da kyakkyawan sakamako, inda tuni aka koma ayyuka, da sarrafa hajoji a masana'antu. Kaza lika makarantu, kama daga jami'o'i, da na midil, da firamare, duk sun koma gudanar da darussa.

A cewar jaridar "Newsweek" ta Amurka, wani taron shakatawa da mazauna birnin Wuhan suka gudanar cikin wurin ninkaya a watan da ya gabata, ya tabbatarwa duniya cewa, yanayin da Sin ke ciki game da wannan cuta ya banbanta da halin da ake ciki a Amurka, da India da sauran kasashen duniya. Mujallar ta ce nasarar da Sin ta cimma a wannan fanni na da nasaba da sahihan matakai, kuma masu tsauri da gwamnatin kasar ta aiwatar, baya ga amincewar da al'ummun kasar suka nuna ga gwamnatin su.

A nata bangare, jaridar "Bangkok Post" ta kasar Thailand, ta wallafa wani rahoto mai taken "Ta yaya Sin ta kai ga dakile wannan annoba?" Rahoton ya lasafta wasu ginshikai guda 3, wadanda suka ba da damar cimma manyan nasarori cikin watanni 3 kacal, ciki kuwa hadda batun managarcin jagoranci, da bin cikakkun ka'idojin kandagarki da shawo kan cutar, da kuma tallafawa manufar hakan daga dukkanin bangarori.

Rahoton ya kuma ce, managarcin jagoranci da JKS ke bayarwa, ya tabbatar da nasarar ayyukan yaki da annobar, da mikewa kan turba ta gari bisa tsari. A daya bangaren kuwa, dalilin da ya sa Amurka ta zamo kasa mafi shan fama da wannan annoba shi ne, gwamnatin shugaba Donald Trump, ta gaza wajen samar da sahihin jagoranci a fannin yaki da wannan annobar.

Har ila yau, rahoton jaridar, ya jaddada muhimmancin hada aikin shawo kan wannan annoba da na kandagarkin ta. Bugu da kari, Sinawa sun fahimci yanayin da ake ciki, sun kuma ba da goyon baya ga gwamnati. Kaza lika rahoton ya nuna yadda ayyukan yaki da cutar COVID-19 ya zamo yaki na daukacin kasa, wanda ya shafi kowa da kowa.

Bisa fahimta da hadin kan daukacin al'ummun kasar Sin, su kimanin biliyan 1.4, gwamantin kasar ta kai ga aiwatar da cikakkun matakai na kandagarki da shawo kan wannan annoba yadda ya kamata. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China