Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uwargida Peng Liyuan ta taya murna ga lambar yabon ba da ilmi ga 'yan mata da mata ta UNESCO
2020-10-12 21:02:12        cri

Yau uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma manzon musamman ta hukumar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'adu wato UNESCO kan aikin ingiza aikin ba da ilmi ga 'yan mata da mata Peng Liyuan ta taya murna ta kafar bidiyo ga lambar yabon ba da ilmi ga 'yan mata da mata karo na 5 na hukumar.

Uwargida Peng Liyuan ta taya wadanda suka samu lambar yabo murna da suka fito daga kasashen Sri Lanka da Kenya, inda ta bayyana cewa, a shekarar 2015, kasar Sin da hukumar UNESCO sun kirkiro da lambar yabo cikin hadin gwiwa. Galibi a kan ba da lambar yabon ne ga wadanda suka taka rawar gani wajen taimakawa 'yan mata da mata samun ilmi da kwarewar aiki da cimma burinsu ta hanyar daukar hakikanin matakai, haka kuma su kan taimaka wajen inganta daidaiton jinsi da ci gaban zaman takewar al'umma.

Uwargidan ta kara da cewa, kaso 63 bisa dari na wadanda ba su iya karatu da rubutu ba a fadin duniya mata ne, idan mata ba su samu ilmi yadda ya kamata ba, to zai yi wahala al'ummu ta samu ci gaba, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da shirya aikin ba da lambar yabon ba da ilmi ga 'yan mata da mata tare da hukumar UNESCO, tare kuma da ingiza cudanya da hadin gwiwa a fuskar ba da ilmi a tsakanin kasa da kasa, kana za ta kara yin kokari domin kyautata aikin ba da ilmi ga 'yan mata da mata, ta yadda za ta taka rawa wajen tabbatar da muradun samun ci gaba mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030.

Babban darektar hukumar UNESCO Audrey Azoulay ta yaba da gwamnatin kasar Sin ta kuma nuna godiya bisa ga goyon bayan hukumar na kirkiro lambar yabon, kuma ta ba da gudummawa wajen ingiza daidaiton jinsi, ta kuma bayyana cewa, hukumarta za ta yi kokari tare da bangarori daban daban domin samar da damammakin samun ilmi da makoma mai haske ga 'yan mata da mata a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China