Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Madam Peng Liyuan ta amsa wasikar da 'yan makarantar Sri Lanka suka aika mata
2020-03-03 21:18:40        cri
A jiya Litinin, uwargidan shugaban kasar Sin, Madam Peng Liyuan ta amsa wasikar da daliban makarantar Devi Balika Vidyalaya ta kasar Sri Lanka suka aika mata, inda ta bayyana godiyarta dangane da yadda daliban suka nuna goyon baya ga kasar Sin a kokarinta na dakile cutar numfashi ta Covid-19, ta kuma ba su kwarin gwiwar ba da gudummawarsu ga karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Makarantar Devi Balika Vidyalaya shahararriyar makaranta ce da gwamnati ta kafa, wadda ke da dalibai kimanin dubu biyu. A kwanan baya, wakilan dalibai 43 na makarantar suka aikawa Madam Peng Liyuan wata wasika da wani zane, don bayyana goyon bayansu ga kasar Sin a kokarinta na shawo kan wannan annoba.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China