Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu adadi mafi yawa na wadanda COVID-19 ta yi ajalinsu cikin rana 1 a Iran
2020-10-12 10:54:46        cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Iran, ta sanar da mutuwar mutane 251 sanadiyyar cutar COVID-19 a jiya Lahadi, wanda ya kasance adadi mafi yawa cikin kwana 1, tun bayan barkewar cutar a kasar.

Kakakin ma'aikatar, Simi Sadat Lari ce ta bayyana haka, yayin taron manema labarai da ta kan yi a kullum, inda ta ce adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu a kasar ya karu zuwa 28,544.

Sima Lari, ta ce hukumomi sun gano sabbin mutane 3,822 da suka kamu da cutar a ranar jiyan, wanda ya kawo jimilar wadanda cutar ta harba a kasar zuwa 500,075.

Ta kara da cewa, mutane 406,389 sun warke daga cutar, kuma kawo yanzu an sallamesu, yayin da wasu 4,482 ke sassan kula da marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani.

Har ila yau, ta ce zuwa yanzu, an gudanar da gwaje-gwajen cutar 4,312,514 a kasar ta Iran.

A tsakiyar watan Fabreru, yayin da cutar ke matakin farko na barkewa a kasar Sin, Iran ta kunna Fitilar hasumiyar 'yanci ta Azadi dake Tehran, domin nuna goyon bayanta ga kasar Sin, sannan ta ba kasar gudunmmuwar marufin baki da hanci miliyan 3.

Ita ma a nata bangare, kasar Sin, ta aike da kayayyakin kiwon lafiya da dama zuwa Iran. Ko a ranar 29 ga watan Fabreru, tawagar kwararrun jami'an lafiya na kasar Sin kunshe da mutum 5, ta ziyarci Iran, inda ta yi aiki na tsawon wata guda domin taimakawa kasar yaki da annobar, (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China