Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fashewar gas ta hallaka a kalla mutum 4 a Lagos
2020-10-08 20:37:47        cri
Rahotanni daga jihar Lagos dake kudancin Najeriya, na cewa wata fashewar iskar gas da ta auku a wani gidan mai, ta hallaka a kalla mutane 4 a Alhamis din nan. Kaza lika hadarin ya rutsa da mutane da dama, wadanda aka ceto daga inda fashewar ta auku.

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Nosa Okunbor, ya ce fashewar ta auku ne da misalin karfe 6 na safe, lokacin da mutane ke shirin fita harkokin su na yau da kullum, a unguwar Baruwa mai cunkoson jama'a, daura da titin Ipaja.

Mr. Okunbor ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kawo yanzu ba a tantance musabbabin aukuwar fashewar ba, ko da yake an fara gudanar da bincike. Ya ce gidan man ya jima yana sayar da iskar gas da ake amfani da ita wajen girki a gidaje.

Su ma wasu mazauna unguwar sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna cike da fargabar samun karin asarar rayuka masu yawa, sakamakon maida hankali da jami'an ceto ke yi wajen kashe wutar da ke ci ganga-ganga a gidan man, maimakon wadda ta kama gidajen dake daura da shi.

Gidaje da dama dai sun kama da wuta, yayin da kuma jami'an aikin ceto ke ta kokarin tseratar da rayuka da dukiyoyin da gobarar ta shafa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China