Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya za ta magance rashin da'a da 'yan sanda ke aikatawa
2020-10-06 15:36:12        cri
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bayyana kudirin kasarsa na yiwa matakan yaki da manyan lafuffuka gyaran fuska da rage ayyukan rashin da'a da wasu sassa na 'yan sandar kasar ke aikatawa.

Mohammed Adamu wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa, ya kuma haramta ayyukan rundunonin musamman da aka kafa, ciki har da rundunar tarayya ta musamman dake yaki da ayyukan fashi da makami(FSARAS) , da rundunar dabarun musamman(STS) da rundunar binciken bayanan sirri (IRT), da sauran rundunoni, daga kafa shingayen sintiri a sassan kasar.

Bugu da kari, rundunonin da wannan umarni ya shafa, wadanda ba su da iznin gudanar da sintiri a kan hanyoyin kasar, ba a kuma yarda su rika gudanar da ayyuka kamar dakatarwa da binciken ababan hawa a shingayen binciken ababan hawa ba, da kafa shingayen bincike da ma binciken ababan hawan.

A cewar sanarwar, haramci na zuwa ne, bayan binciken da rundunar 'yan sandan kasar ta gudanar, wanda ke nuna cewa, wasu jami'an irin wadannan rundunoni da aka haramta, na fakewa da kayan sarki wajen gudanar ayyukan da suka saba doka.

An sha samun rahotanni a watannin baya-bayan nan, kan yadda 'yan sanda ke cin zarafin jama'a, da karbar na goro, lamarin da jama'a suka koka a kai.

Jama'a da dama dai sun yi Allah wadai da wannan lamari, ciki har da mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo. A cewar jaridar Nation da ake wallafawa a kasar, Osinbajo, ya shaidawa manema labarai cewa, yana goyon bayan haramcin da babban sifeton 'yan sandan kasar ya dauka kan rundunar FSARS da makamantansu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China