![]() |
|
2020-10-08 15:46:30 cri |
Wani rahoton hadin gwiwa na UNECA, da hukumar yaki da fatara ta "anti-poverty organization ONE", ya nuna irin mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta haifar, a fannin aikewa da kudade zuwa sassan Afirka, wanda hakan ke da nasaba da halin da 'yan ci ranin nahiyar ke ciki a kasashen ketare.
Rahoton mai taken "kare kudaden da ake aikewa gida, a yayin da ake fama da cutar COVID-19" ya yi nuni da karuwar irin wadannan kudade cikin gwamman shekarun da suka gabata, in ban da shekarar nan ta 2020, kuma irin wadannan kudade su ne ginshikin kudaden da nahiyar ta fi samu daga ketare, sama da na tallafin da kasashen ketare ke samarwa nahiyar, da kudaden da sassa masu zaman kan su ke shigarwa nahiyar, da ma na jarin kai tsaye na ketare.
Rahoton ya kuma ce, cutar COVID-19 ta gurgunta harkokin tattalin arzikin duniya, wanda hakan ya sanya aka yi hasashen raguwar kudaden da ake aikewa Afirka da kaso 21 bisa dari a bana. Akwai kuma tabbacin cewa, al'ummun dake dogaro da irin wadannan kudade, za su fuskanci karancin su a shekarar ta bana. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China