2020-09-21 10:50:37 cri |
Jami'in na MDD yace, idan aka dubi yanayin da duniya take a halin yanzu, a bayyane take cewa duk wani kyakkyawan abu na gama gari ana iya samunsa ne ta hanyar kara yin hadin gwiwar kasa da kasa.
Babban sakataren ya kuma yi jawabi game da babbar gudunmawar da kasar Sin ke bayarwa wajen shawo kan kalubalolin duniya da kuma nasarorin da kasar ta samu a yaki da fatara.
Guterres ya bayyana kasar Sin a matsayin "Jigon hadin gwiwar bangarorin daban daban," jami'in MDD yace Sin tana ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin shiyya, da al'amurran kasa da kasa, ya kara da cewa, hadin gwiwar kut-da-kut da MDD ke yi da kasar Sin ya kara fadada zuwa bangarorin wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan duniya, wanda ya hada da nahiyar Asiya, Afrika, da yankin gabas ta tsakiya.(Ahamd)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China