![]() |
|
2020-09-23 09:53:54 cri |
Shugaba Xi ya bayyana haka ne, a jawabin da ya gabatar yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75 wanda aka yi jiya Talata ta kafar dibiyo.
Ya ce, ya kamata a martaba ra'ayin cudanyar bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD. Yana mai cewa, ya zama dole kasa da kasa su kara yin shawarwari da more damammaki tare a yayin da ake tafiyar da harkokin duniya, da shimfida adalci a fannonin da suka shafi kare hakki da samar da zarafi da kuma kafa ka'idoji, ta yadda za'a samu ci gaba cikin lumana da karfafa hadin-gwiwa da cin moriyar juna tare.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China