Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Tsarin gurguzu mai halin musamman na Sin ya cimma nasarorin kawar da kangin talauci
2020-09-20 15:38:32        cri
Hasashen masana ya nuna cewa, kasar Sin zata iya cimma nasarar kawar da kangin fatara a tsakanin al'ummarta ya zuwa karshen wannan shekarar duk da kalubalolin annobar COVID-19, wani masanin kasar Cuba ne ya bayyana hakan.

"Cikin wasu 'yan gwamman shekarun da suka gabata kasar Sin ta yi aiki tukuru wajen tsame mutane kusan miliyan 800 daga kangin talauci, wanda hakan wata alama ce dake nuna karfin hali da jajurcewar da kasar ke da shi wajen tinkarar kalubalolin duniya", in ji Eduardo Regalado, wani babban masani a cibiyar nazarin siyasar kasa da kasa dake Havana.

Masanin na kasar Cuba ya ce, kasar Sin ta baiwa duniya gudunmawar rage kaifin talauci da kashi 70 bisa 100 a kokarin cimma muradun MDD na samar da dawwaumammen ci gaba nan da shekarar 2030, masanin wanda ya bayyana hakan a wata zantawar da ya yi da manema labarai gabanin gudanar da bikin cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Cuba, wanda zai gudana a ranar 28 ga watan Satumba.

Ya ce samakon da kasar Sin ta cimma na yaki da talauci ya tabbata ne bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ita ce jigon nasarorin da gwamnatin Sin da al'ummar Sinawa suka samu.

Regalado ya ce, tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ya cimma manyan nasarorin kawar da kangin talauci, da kawo kyakkyawar makoma, gami da kyautata zaman rayuwar dukkan al'ummar Sinawa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China