Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Cuba ya yi kira ga jama'arsa da su hada kai don tinkarar shingen da Amurka ta sanyawa kasar
2019-12-22 16:44:21        cri
Shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel Bermúdez a jiya Asabar ya bayyana cewa, shingen da kasar Amurka ke kara sanyawa kasarsa ya riga ya kawo tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar, kamata yayi jama'ar kasar su hada kai don fuskantar matsin lamba a fannin tattalin arziki sakamakon shingen da Amurka ta kafa.

Shugaban Cuban ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa yayin rufe taro karo na hudu na babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Cuba karo na 9, inda ya waiwayi jerin matakan kakaba takunkumi da gwamnatin kasar Amurka ta dauka a bana a fannonin yawon shakatawa na Cuba, da hana shigo da man fetur da Cuba ke yi, da kawo cikas ga hada hadar kudin Cuba da harkokin bankunan kasar da dai sauransu. Ya ce, kasar Cuba ta fuskanci wahalhalu a wannan shekara, "babu wani fannin da ya tsira daga illolin Amurka", kasar Amurka ta yi niyyar hambarar da gwamnatin kasar Cuba ne ta hanyar lalata tattalin arzikin kasar.

Baya ga haka, shugaban ya yi kira ga jama'arsa da su hada kai don kawar da mawuyacin halin da kasar ke ciki. Ya kuma jaddada cewa, akwai bukatar Cuba ta bunkasa samar da kayayyaki, da inganta iri da inganta kayayyakin da take samarwa, don rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ketare. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China