Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin ta la'anci ziyarar da jami'in Amurka zai kai yankin Taiwan
2020-09-17 19:41:12        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin tana adawa da ma yin Allah wadai da kakkausar murya, kan ziyarar da mataimakin sakataren raya tattalin arziki, makamashi da muhalli na kasar Amurka Keith Krach zai kai yankin Taiwan na kasar Sin.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Wang Wenbin, shi ne ya bayyana haka, inda ya bukaci bangaren Amurka da ya mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya, da ma sanarwowin hadin gwiwa guda uku tsakanin Sin da Amurka. Wang ya ce, ziyarar ta keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma wadancan sanarwowi uku da sassan biyu suka cimma a tsakaninsu, a don haka bangaren kasar Sin ya gabatar da kokensa ga bangaren Amurka.

Jami'in ya nanata cewa, Taiwan wani bangare na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. A don haka ya bukaci bangare Amurkaļ¼Œda ya hanzarta dakatar da yin mu'amalar jami'ai da yankin Taiwan da ma duk wasu harkoki da suka shafi yankin. Ya kuma yi gargadin cewa, kasar Sin, za ta dauki matakan da suka dace bisa yanayin da ake ciki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China