Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta yi kusan kawo karshen annobar COVID-19
2020-09-18 10:56:02        cri

Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Alhamis cewa, bisa ga irin matakan da kasar ta dauka na yaki da annobar COVID-19, a yanzu haka, annobar tana shirin ban kwana daga kasar.

A jawabin da kwamitin yaki da annobar COVID-19 na ofishin shugaban kasar wato PTF, wanda ya saba gabatarwa a kullum a Abuja, shugaban kwamitin kana sakataren gwamnatin tarayyar Boss Mustapha ya ce, an samu gagarumar nasara a yaki da annobar, kuma a yanzu an fara ganin alamun kawo karshen annobar a kasar.

Mustapha ya kara da cewa, sai dai kuma, kamar yadda suka saba fada a kowane lokaci, za su yi taka tsan tsan wajen kiyaye wadannan nasarorin da aka cimma.

Ya ci gaba da cewa, kwamitin na PTF, yana ci gaba da sanya ido da lura game da halin da ake ciki a filayen jiragen saman kasar, kasancewar kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika a kwanan baya ta sanar da sake bude filayen jiragen samanta na zirga zirgar kasa da kasa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China