Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya jaddada bukatar daidaita sha'anin cinikayyar waje da zuba jari
2020-06-29 10:53:30        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar ci gaba da daukar matakai don habaka bude kofarta ga ketare da kuma daidaita sha'anin cinikayyar waje, da bunkasa zuba jari.

Li ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin wani taron musayar fahimta da ya hallara jami'an gwamnati da jagororin kamfanonin kasar, inda ya ce daukar wadannan matakai na da matukar muhimmanci wajen daidaita yanayin tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi.

Firaministan ya kara da cewa, yanayin hada hadar cinikayyar waje zai ci gaba da kasancewa mai sarkakiya da rudani, a gabar da cutar COVID-19 ke kara bazuwa a sassan duniya, take kuma kara tura tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali, yayin da kuma a hannu guda tattalin arzikin kasar Sin ke zurfafa hadewa da na sauran sassan duniya.

Mr. Li ya kara da cewa, akwai bukatar tabbatar da daidaito a sassa 6, da samar da tabbaci a bangarori 6, yayin da ake aiwatar da kudurorin zurfafa bude kofa.

Sassan 6 dai sun hada da na samar da ayyukan yi, da fannin hada hadar kudi, da cinikayyar waje, da zuba jarin waje, da fannin jarin cikin gida, da lura da abun da-ka-je-ya-zo.

Bangarorin 6 kuwa su ne na wanzar da ayyukan yi, da biyan bukatun al'umma na yau da kullum, da inganta harkokin kasuwanni, da samar da isashen abinci da makamashi. Sauran su ne daidaita harkokin masana'antu da na samar da hajoji, da inganta ayyukan hukumomi a mataki na farko. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China