Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Ambaliyar ruwa ta kashe rayuka 102 a Sudan, ta shafi mutane kusan 720,000
2020-09-15 10:59:11        cri
Hukumar kula da jin kai ta MDD ta sanar a ranar Litinin cewa, adadin mutanen da ambaliyar ruwa a Sudan ta shafa ya karu da 160,000 a cikin kwanaki hudu zuwa kusan 720,000, yayin da rayukan 102 suka salwanta.

Ofishin shirin ayyukan jin kai na MDDr OCHA ya sanar da cewa, sama da gidaje 71,000 ne suka rushe, yayin da wasu karin gidajen 72,000 suka lalace, sannan sama da dabbobi 3,300 ambaliyar ruwan ta kashe.

Ofishin na OCHA ya ce, gwamnatin kasar, da hukumomin MDD, da kungiyoyi masu zaman kansu sun kai dauki da tallafin kayan abinci da na kiwon lafiya da sauransu ga mutane kimanin 200,000.

Hukumar dake kula da hasashen yanayi ta fitar da wani gargadi na yiwuwar samun mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa har zuwa ranar Talata, ko da yake, tashoshin dake sanya ido kan tekun Blue Nile sun samu raguwar ruwan tekun da mataki milimita 3 a karshen makon da ya gabata. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China