Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren AL ya sake nanata martaba "shirin shimfida zaman lafiya na Larabawa"
2020-09-10 13:46:18        cri

Jiya Laraba Ahmed Aboul-Gheit, babban sakataren kawancen kasashen Larabawa wato AL ya ce, "shirin shimfida zaman lafiya na Larabawa", babbar manufa ce ta shimfida dawamammen adalci da zaman lafiya daga dukkan fannoni a tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila.

A wannan rana kwamitin ministocin harkokin wajen AL ya kira taro karo na 154 ta kafar intanet, inda aka tattauna tasiri da yarjejeniyar dawo da huldar da ke tsakanin Isra'ila da hadaddiyar daular Larabawa yadda ya kamata za ta yi kan halin da ake ciki a yankin, da kuma batun Palasdinu da Isra'ila. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China