Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin masu cutar COVID-19 guda 49 a babban yankin kasar Sin
2020-08-10 16:20:48        cri

Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, ta samu rahoton sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 kimanin 49 a babban yankin kasar Sin a ranar Lahadi, wanda ya kunshi mutane 35 da suka fito daga kasashen ketare sai kuma mutane 14 da suka kamu da cutar a cikin gidan kasar.

Dukkan mutanen 14 da suka harbu da cutar a cikin gida an same su ne a jahar Xinjiang, kamar yadda hukumar lafiyar kasar ta sanar cikin bayanan da take fitarwa a kullum game da cutar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China