Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya mika lambobin yabo ga wadanda suka taka rawa a yaki da COVID-19
2020-09-08 14:02:05        cri

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika lambobin yabo ga wadanda suka lashe lambar yabo ta Jamhuriya da karramawa ta kasa, saboda gagarumar gudummawar da suka bayar a yakin da kasar ta yi da annobar COVID-19.

A jawabin da ya gabatar yayin taron da ya gudana a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, shugaba Xi ya ce, kasar Sin ta sake taka rawar gani a yakin da bil-Adama ke yi da cututtuka. Shugaban ya takaita ruhin kasar Sin na yaki da annobar COVID-19, wadda ke nuna muhimmancin rayukan jama'a, da kishin 'yan kasa baki daya suka nuna, da sadaukarwa, da mutunta shawarwarin kimiya da mutunta daukacin bil-Adama.

Xi ya ce, kasar Sin ta kuma taimaka wajen ceton dimbin rayuka daga annobar COVID-19 a sassa daban-daban na duniya ta hanyar daukar managartan matakai. Ya kuma jaddada cewa, nuna son kai, da dorawa wasu laifi, da jirkita gaskiya da karya, ba kawai za su illata kasa da al'ummarta ba, amma za su illata al'ummomin duniya baki daya. A don haka ya bukaci, da a kara zage damtse, don ganin bayan wannan annoba. Shugaba Xi ya ce, babu wanda zai hana al'ummar Sinawa samun rayuwa mai inganci. Hakika kasar Sin da al'ummarta, za su yi nasara a gwargwaryar da suke a yi a sabon zamani.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China