Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufofin Sin za su bunkasa harkokin cinikayya da kyautata makomar tattalin arzikin duniya
2020-09-05 20:50:38        cri

A lokacin kaddamar da taron bajekolin ayyukan ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020, wanda ya gudana a ranar 4 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wasu muhimman shawarwari uku game da hadin gwiwa a fannin kamfanonin ayyukan hidima, a jawabin wanda ya gabatar ta kafar bidiyo, ya sanar da kudurin kasar Sin na yin hadin gwiwa kan batun. Akwai jerin matakai da za'a dauka wadanda za su tabbatar da aniyar kasar Sin na zurfafa manufar bude kofarta ga ketare, ko shakka babu, wannan mataki zai kara ingiza samun tabbaci da karfin samun bunkasuwar ci gaban duniya.

Kasancewar shi ne babban taron ciniki da tattalin arziki na kasa da kasa irinsa na farko da aka gudanar a kasar Sin ta kafar intanet da ma na zahiri tun bayan barkewar annobar COVID-19, taron bajekolin ayyukan hidimomin ya ja hankalin kamfanoni da cibiyoyi 18,000 daga kasashen duniya da shiyyoyi kimanin 148, kuma sama da mahalarta 100,000 ne suka yi rijistar shiga taron.

A jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da cikakken sharhi game da kalubaloli da kuma damammakin dake fuskantar tattalin arzikin duniya a halin yanzu, kana shugaban ya zayyana hanyoyin da za su zama mafita, yin hadin gwiwa zai iya zama wani muhimmin jigon wanzar da cigaba. A bisa kididdiga, kashi 60% na tattalin arzikin duniya ya ta'allaka ne kan kamfanonin ayyukan hidima, da harkokin hidimar fitar da hajoji zuwa ketare, wanda shi ne kashi 20% na yawan adadin fitar da kayayyaki na duniya, kuma fannin yana bayar da gudunmawar kusan kashi hamsin bisa dari na kudaden shiga daga fannin harkokin kasuwancin kasa da kasa.

Yayin da duniya ke fuskantar tasirin annobar COVID-19, ta yaya za a bunkasa hadin gwiwa a fannin kamfanonin hada hadar ayyukan hidima ta yadda zai samar da babbar moriya wajen daga matsayin ci gaban tattalin arzikin duniya? Xi Jinping ya gabatar da wasu shawarwari uku game da wannan batu, inda ya yi kira ga kasa da kasa da su hada kai don samar da wani muhallin hadin gwiwa, su hada gwiwa wajen farfado da ayyukan dake shafar kirkire-kirkiren fasahohi, kana su hada gwiwa wajen samar da yanayin mu'amala bisa tsarin cin moriyar juna karkashin hadin gwiwa.

A matsayinsa na babban jagoran fadada manufar bude kofa, shugaban kasar Sin ya kuma ayyana jerin matakan da kasar ta Sin za ta kara bude kofarta ga waje karkashin hadin gwiwar kamfanonin hada-hadar ayyukan hidima, hakan ya kara haskawa duniya cewa, har kullum, kasar Sin burinta shi ne ta zamanto mai bada jagorancin kara ingiza manufar bude kofa na kasa da kasa, kuma ta kasance cikakkiyar mai goyon bayan tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban a tsarin cinikayyar duniya.

Bude kofa a tsarin cudanyar tattalin arzikin duniya zai samar da makoma mai haske, yayin da rufe kofar zai haifar da koma baya. Wannan shi ne hakikanin yadda tsarin dokar halayyar ci gaban bil Adama take. Domin kiyayewa da mutunta wannan tsarin doka, har kullum kasar Sin tana daukar kwararan matakan kara bude kofarta ga tsarin tattalin arzikin duniya, kuma tana ci gaba da nacewa kan manufarta na karfafa hadin gwiwa da al'ummar duniya domin a gudu tare a tsira tare don samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China