Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Idan Bikin CIFTIS Ya Ci Nasara Za A Inganta Sabon Salon Raya Tattalin Arziki Mai Bude Kofa Ga Waje
2020-09-05 20:39:17        cri

Kwanan baya, daliban sassan kasar Sin sun koma makarantunsu bayan sun kwashe rabin shekara suna karatu daga gida. Cikin wannan rabin shekara da ta gabata, cutar numfashi ta COVID-19 ta koyar da mu wani muhimmin darasi, inda ta sa aka maida hankali matuka kan komawar dalibai makarantu.

A hakika dai, tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Sin suna ci gaba da farfadowa sakamakon matakan kandagarki da aka dauka a yau da kullum, mutanen kasar sun gaggauta dawowa bakin ayyukansu domin inganta bunkasuwar tattalin arziki cikin yanayin zaman karko, wajen inganta bunkasuwar harkokin kasa kamar yadda ake fata.

A wannan mako, an bude bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020, CIFTIS wanda ya janyo hankulan kasa da kasa. A matsayin bikin dake kan gaba a wannan fanni, wannan shi ne bikin cinikayyar kasa da kasa mafi muhimmanci da kasar Sin ta gudanar, kuma karo na farko, bayan ta cimma nasarar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. A bana, an tsara hanyoyi da dama wajen gudanar da wannan biki, domin biyan bukatun yin kandagarkin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma. Haka kuma, ya nuna aniyar kasar Sin wajen habaka sana'o'in ba da hidima, yayin da take kara bude kofa ga waje.

Ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen karfafa aikin yin kwaskwarima da kara bude kofa ga waje, koda yake ana fuskantar kalubalen sauye-sauyen yanayi da matsaloli da dama. Idan mun gane muhimmiyar ma'anar wannan batu, za a gane cewa, idan aka gudanar da bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2020 cikin nasara, zai ci gaba da inganta sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje, ta yadda cinikayyar ba da hidima za ta ba da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki da kuma kyautata sabon tsarin neman bunkasuwa ta hanyar bude kofa ga waje daga dukkan fannoni. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China