![]() |
|
2020-08-29 20:58:31 cri |
Shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun manufofin jam'iyyar JKS mai mulkin kasar kan sha'anin shugabancin jahar Tibet a sabon zamanin da muke ciki.
Xi ya bukaci a kara himmatuwa don tabbatar da tsaron kasa da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali, da inganta zaman rayuwar al'umma, da samar da ingantaccen yanayi, kana samar da kyakkyawan tsari don tsaron kan iyakokin kasar da nufin tabbatar da tsaro.
Tilas ne a yi kokarin gina sabon tsarin gurguzu ga jihar Tibet domin dunkulewarta, da samun ci gaba, da bunkasa al'adu, da samar da zaman lafiya da kayata yankunanta, in ji shugaba Xi. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China