Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Kenya: ziyarar Mike Pompeo a arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya ba ta da ma'ana
2020-08-30 17:27:18        cri

Kwanan baya, Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya kammala ziyararsa a arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya. Wani masanin kasar Kenya ya yi nuni da cewa, yunkurinsa na karfafa tasirin Amurka a Afirka ba shi da ma'ana, ba zai samu sakamako ba.

A lokacin ziyarar Mike Pompeo, karo na farko ne sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci kasar Sudan cikin shekaru 15 da suka wuce. Alex Awiti, mataimakin shugaban kula da harkokin ba da ilmi na jami'ar Aga Khan na Kenya yana ganin cewa, Sudan ta yi kama da wata gada ce da ta hada arewacin Afirka da yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. Amurka tana yunkurin shawo kan kasashen Afirka da su goyi bayanta a wasu al'amuran kasa da kasa. Amma Mike Pompeo ya yi wannan ziyara ne domin samun muradun siyasa, ziyararsa ba ta da ma'ana.

A ganin masanin, tun daga karni na 21 har zuwa yanzu, Amurka na yunkurin karfafa tasirinta a Afirka, ta tilasta wa kasashen Afirka su bi tsarin dimokuradiyya irin nata, wanda bai dace da Afirka ba. A sa'i daya kuma, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka ya fi cancantar ci gaban kasashen Afirka. Ko da yake akwai nisa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, amma sun kulla kyakkyawar makwabta a tsakaninsu. Sin na goyon bayan Afirka a fannin samar da ababen more rayuwar jama'a. Su aminai ne dake yin zaman daidai wa daida. Suna mutunta juna ta fuskar al'adu. Suna kuma goyon bayan juna wajen cimma buri. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China