Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin FAO: yanayin tsaron abincin Kenya bai canja ba, duk da COVID-19
2020-08-28 10:36:56        cri
Wakilin hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) a kasar Kenya, Tobias Takavarasha, ya bayyana cewa, yanayin tsaron abinci a kasar ta Kenya bai canja ba, duk da tasirin annobar COVID-19.

Tobias ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a Nairobiļ¼Œfadar mulkin kasar ta Kenya yayin taron kaddamar da tsare-tsaren daidaita rigingimu cewa, mahukuntan kasar sun dauki matakan da suka dace a kan lokaci, don taimakawa masu sayayya rage radadin da za su iya fuskanta.

Jami'in ya bayyana cewa, 'yan kasar sun yi kyakkyawan amfani da tsame sashe aikin gonan kasar daga haramcin da aka sanya masa a baya, don rage yaduwar cutar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China