Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin amintacciyar abokiya ce ta Sudan ta Kudu
2020-08-21 13:52:59        cri

A kwanakin baya, tawagar masanan likitoci zuwa kasar Sudan ta Kudu da gwamnatin kasar Sin ta tura ta isa birnin Juba, don samar da gudummawa wajen yaki da cutar COVID-19 a kasar, bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi mata. Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Hussein Abdelbagi ya bayyana cewa, kasar Sin amintacciyar abokiyya ce ta kasar Sudan ta Kudu a yayin tinkarar matsala.

Gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar masanan likitoci ta yaki da cutar COVID-19 zuwa kasar Sudan ta Kudu, wadda hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta kafa, kuma kwamitin kiwon lafiya na lardin Anhui ya zabi masana 8 a fannonin kula da cututtuka masu yaduwa, da magance kamuwa da cututtuka masu yaduwa, da ilmin numfashi, da kula da wadanda suka kamu da cututtuka masu tsanani, da yin bincike, da kuma ba da kulawa ga wadanda suka kamu da cutar da sauransu.

Shugaban tawagar masanan, kuma shugaban asibiti na farko mallakar jami'ar ilmin likitanci ta lardin Anhui Liang Zhaozhao ya yi bayani da cewa, a yayin da tawagar ke aiki a kasar Sudan ta Kudu, masanan za su yi musayar fasahohi da ra'ayoyi tare da hukumomin kasar, da kuma na kasa da kasa masu nasaba da aikin. Za su kuma ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya dake kasar, da horar da likitoci a wurin, da kuma samar da gudummawa ga hukumomin masu jarin kasar Sin a kasar.

Liang Zhaozhao ya bayyana cewa, "Muna shirin yin aiki a kasar Sudan ta Kudu har na tsawon kwanaki 10, muna son ganin yanayin yaduwar cutar COVID-19, da yadda ake magance yaduwar ta a kasar, kana muna da shirin more fasahohin yaki da cutar na kasar Sin, tare da horar da jami'an hukumomin da abin ya shafa a wannan fanni."

Mr Liang ya bayyanawa 'yan jarida cewa, bayan da tawagar ta isa kasar Sudan ta Kudu, masanan sun yi fatan ziyarta, da gudanar da bincike a wurare mafiya taruwar mutane, kamar filin jiragen sama, da kasuwanni da sauransu.

Liang ya bayyana cewa, "Bayan da muka isa kasar Sudan ta Kudu, da farko mun yi bincike kan yanayin magance yaduwar cutar COVID-19 a filin jiragen sama. Jiya da yamma, mun ziyarci kasuwa mafi girma ta kasar, don yin binciken yanayin kasuwar wajen magance yaduwar cutar. Yau da safe mun yi mu'amala tare da masanan kasar da wannan batu ya shafa."

A jiya ne, mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Hussein Abdelbagi ya gana da dukkan membobin tawagar masanan na Sin, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, yayin da Sudan ta Kudu ke fuskantar matsaloli da fama da mawuyacin hali, Sin ta samar da gudummawa da farko gare ta. Bayan da aka gamu da yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar, kasar Sin ita ce ta farko da ta samar da kayayyakin yaki da cutar cikin gaggawa ga Sudan ta Kudu, don haka amintacciyar abokiya ce ga kasar Sudan ta Kudu.

Ya ce yana matukar farin ciki da ganin Sudan ta Kudu da Sin na raya dangantakar abokantaka, da sada zumunta a tsakaninsu, wanda hakan zai amfani jama'arsu baki daya. Abdelbagi ya kara da cewa, tura tawagar masanan yaki da cutar COVID-19 da Sin ta yi ya shaida cewa, Sin ta dora muhimmanci ga zumunta, da huldar dake tsakaninta da kasar Sudan ta Kudu. Yana kuma fatan masanan Sin za su more fasahohin yaki da cutar, don taimakawa horar da likitocin kasarsa, wajen inganta karfin tinkarar cutar a kasar.

Ya kara da cewa, Sin da Sudan ta Kudu kamar iyali guda ne, kuma yana fatan masanan Sin za su yi aiki kamar a garinsu, yayin da gwamnatin Sudan ta Kudun za ta samar da sauki ga ayyukan masanan a dukkan fannoni.

Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta Kudu ta gabatar, an ce, yawan mutanen da aka tabbata sun kamu da cutar COVID-19 a kasar a halin yanzu ya kai 2494, a cikinsu mutane 47 sun mutu, kana akwai kuma mutane 1290 da suka warke daga cutar.

Liang Zhaozhao ya bayyana cewa, Sudan ta Kudu ta fuskanci yanayin yaki da cutar mai tsanani. Ana kuma bukatar kafa tsari na yaki da cutar, kuma ya kamata hukumomi daban daban su yi hadin gwiwa, don tawagar masanan Sin ta gabatar da damar more fasahohin yaki da cutar ga kasar Sudan ta Kudu. Ya ce, "Mun san akwai doguwar hanya ta cimma nasarar yaki da cutar a kasar Sudan ta Kudu. Ana bukatar kara daukar matakai don magance yaduwar ta. Za mu yi bayani ga hukumomin da abin ya shafa na kasar, don taimaka musu wajen kara fahimtar dabarun yaki da cutar, da kuma inganta karfin yaki da ita." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China