Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Austriliya: akwai alaka tsakanin bayanan bogi da suka samo asali daga Intanet game da annobar COVID 19 da masu adawa da bunkasuwar kasar Sin
2020-06-12 13:49:18        cri

Kwanakin baya, cibiyar nazari ta Autriliya ta ba da wani rahoto mai jigon "kamar kwayar cuta: tsara yaduwar bayanan bogi game da COVID-19". Rahoton ya bayyana cewa, tun daga watan Maris na bana, an yi ta yayata bayanan bogi a kafar Twitter da sauran kafofin Intanet yayin da ake fama da COVID-19, wadanda ke cewa, wai gamnatin kasar Sin ta kirkiro wannan kwayar cuta a kwalejin nazarin kwayoyin cuta dake birnin Wuhan, matakin dake da alaka kut da kut da wadanda ba su son ganin bunkasuwar kasar Sin ko kadan, da kuma nuna adawa ga samar da allurar rigakafin cutar da bunkasuwar fasahar 5G.

Cibiyar nazari ta Austriliya ta nemi masanan jami'ar Queensland da su yi nazari kan bayanai miliyan 2.6 dangane da COVID 19 da aka yayata a Twitter har sau miliyan 25 a karshen watan Maris cikin kwanaki 10, inda suka gano cewa, masu amfani da Twitter fiye da 5700 sun yayata wadannan bayanai har sau 6600 bisa salo iri daya, kuma sun yada jita-jitar cewa, wai gwamnatin kasar Sin ta kirkiro wannan kwayar cutar ta salo iri daya.

Mai nazari Timothy Graham ya nuna cewa, a cikin nazarinsa, ya gano cewa, jita-jita mafi yaduwa a kan Intanet shi ne COVID 19 makami mai guba da aka kirkiro a kasar Sin. Ya ce:  

"Mun sa ido kan jita-jita iri shida da aka yayata a kan Intanet, don nazarin asalinsu da yadda suke yaduwa. Daga cikinsu, jita-jita mafi yaduwa shi ne, na farko wai Bill Gates ya samar da kudaden kirkiro kwayar cutar, na biyu kuwa makami mai guba da Sin ta kirkiro. Mun mai da hankali kan jita-jita na biyu, daga bisani mun gano cewa, akwai wasu kungiyoyi da suka tsai da shirin yayata wannan jita-jita a kan Intanet don ta yadu kamar yadda cutar ke yaduwa."

Ban da wannan kuma, rukunin nazarin ya gano cewa, an yayata yawancin bayanan na Twitter ne cikin sauri. Ko shakka babu, yayata wani bayani cikin sauri na da alaka da wata kungiya. Ya ce:  

"Mun yi nazarin alaka tsakanin bayanan Twitter da yadda aka yayata su, muna ganin cewa, masu amfani da shafin da yawa sun yayata wani bayani cikin dakika daya, abin da ba zai yiwu Bil Adama ya yi ba."

Rahoton ya yi hasashen cewa, wadannan bayanai za su kai ga masu amfani da Twitter daga miliyan 3 zuwa 5, sun yi tasiri matuka.

Dadin dadawa, masu nazarin sun ce, a cikin jita-jita dangane da makami mai guba, kimanin masu amfani da shafin Twitter 2900 da hanyoyin yada bayanai na shafin Intanet fiye da 4000 sun kafa wata kungiya ta yayata bayanai, suna kuma yayata bayanai tsakaninsu ta yadda za su yi tasiri mai yawa. Daga cikinsu kuwa, kashi 2 cikin 3 na da alaka da magoya bayan Donald Trump ko kungiyar QAnon ta masu rajin yayata boyayyun manufofin adawa da gwamnatin Trump da magoya bayansa da kuma jam'iyyar republican. Wadannan shafuka suna bautawa burin siyasa ko tattalin arziki.

Ban da wannan kuma, Timothy Graham ya nanata cewa, mashahuren mutane da kafofin yada labarai na kasa da kasa sun ba da labari kan wadannan bayanai, lamarin da ya sa bayanan suka kara yaduwa. ya ce:

"Muna ganin cewa, bayan wasu mambobin majalisar dokokin kasar Amurka sun yayata jita-jitar makami mai guba, daga baya masu goyon bayan Donald Trump da sauransu sai yayata bayanan da wadannan mambobin suka bayyana bisa tsarin da suka tsayar, abin da ya ja hankalinmu sosai."

A karshe kuma, rahoton ya takaita cewa, wannan kungiya mai baza jita-jita a kan Intanet ta yada jita-jita bisa tsoron jama'a da kuma halayen shafin Intanet ta sada zumunta, har ra'ayinsu sun fi na gwamnatoci da masana karfi, wadanda suke kokarin samar da gaskiya kan lamarin.

MDD ta taba nuna cewa, bayanan bogi na illata kokarin da aka yi na yakar COVID 19 a duniya. Rahoton da cibiyar ta bayar ta amince da wannan ra'ayi, kuma ya nuna cewa, yawancin wadanda suka yayata jita-jitar suna da alaka da kungiyoyin adawa da allurar rigakafi da bunkasuwar 5G, har ma da hana bunkasuwar kasar Sin. Suna fakewa da asalin cutar da illarta da kuma jiyyarta cutar da dai sauransu, don cimma mumunan burinsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China