Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci a yi kaffa-kaffa yayin sake bude makarantun Afrika saboda hadarin cutar COVID-19
2020-08-21 10:47:07        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci kasashen Afrika su dauki kwararan matakan kandagarkin annobar COVID-19 gabanin sake bude makarantun ilmi a kasashen.

Sanarwar da WHO ta fitar a Nairobi ta ce, yayin sake bude makarantun a yankin kudu da hamadar Afrika, ya kamata a dauki matakai da kiyaye ka'idoji domin dakile bazuwar annobar COVID-19.

Daraktar hukumar WHO ta Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce, kamar yadda kasashen ke sake bude harkokin kasuwanci cikin nasara, za a iya sake bude makarantun.

Ta kara da cewa, dole ne a yi la'akari da irin hadarrun dake tattare da daukar wannan mataki domin tabbatar da kare lafiyar yara, da malamai, da iyayen yara, kuma tilas ne a dauki matakai kamar na bada tazara da dai sauransu.

Wani bincike na baya bayan nan da WHO ta gudanar a kasashe 39 na kudu da hamadar Afrika ya nuna cewa, an bude dukkan makarantu a kasashe shida na shiyyar, an rufe dukkan makarantu a kasashe 14, yayin da aka yi kwarya-kwaryar bude makarantun a kasashe 19 na shiyyar domin baiwa dalibai damar rubuta jarrabawa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China