Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Ghana ya mikawa AU ginin sakatariyar AfCFTA
2020-08-18 10:36:05        cri

A jiya Litinin ne shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya mika ginin sakatariyar yarjejeniyar AfCFTA ga kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Da yake gabatar da jawabi yayin mika ginin, shugaba Akufo-Addo ya ce, kasarsa ta sauke dukkanin nauyin dake wuyanta, tana kuma aiwatar da dukkanin kudurorin da aka cimma tsakaninta da hukumar zartaswa ta kungiyar tarayyar Afirka. Don haka ne ma a wannan lokaci ta gabatar da ginin sakatariyar AfCFTA, mai kunshe da dukkanin kayan aiki, a wuri mai tsaro da saukin zuwa, dake shiyyar hada-hadar kasuwanci ta birnin Accra.

Shugaban na Ghana ya ce kasarsa ta yi imanin cewa, karuwar hada-hadar cinikayya daya ne daga manyan hanyoyin zurfafa dunkulewar nahiyar Afirka. Kaza lika hakan zai bunkasa musayar amfanin gona, da hajojin masana'antu, da hada-hadar kudade, da bunkasa binciken kimiyya, da albarkatun fasaha.

Bugu da kari, shugaban ya ce wadannan fannoni za su kara bunkasa moriyar tattalin arzikin nahiyar, da samar da ci gaba, tare da haifar da karin guraben ayyukan yi ga tarin al'ummun nahiyar musamman ma matasa.

Ya ce "Dunkulewar nahiyar Afirka zai kafa wani ginshiki mai karfi, wanda ya wuce batun neman taimako daga ketare, kuma aiwatar da yarjejeniyar AfCFTA zai kawar da tunani da wasu ke yi, cewa kungiyar AU ba za ta iya aiwatar da kudurorin da ta zartas ba. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China