Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xinhua: Afirka ta zama zakaran gwajin dafi a fannin aiwatar da yarjejeniyar cinikayya maras shinge
2019-12-27 10:26:39        cri
Yayin da kariyar ciniki da bin ra'ayin kashin kai ke kara samun gindin zama a sassan duniya masu yawa a wannan shekara ta 2019, kasashen Afirka a nasu bangare, sun kaddamar da yarjejeniyar aiwatar da cinikayya maras shinge tsakaninsu, sun kuma amince da gudanar da cudanya tsakanin sassa daban daban.

Hakan dai na kunshe ne cikin wani sharhi da Zhu Shaobin, masharhanci na kamfanin dillanci labaran Xinhua ya wallafa. Zhu ya ce irin wannan hadin gwiwa na karfafa bunkasa tattallin arzikin yanki ya cancanci yabo, musamman a lokacin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar rashin tabbas, a kuma gabar da masu ra'ayin cudanya da juna, da masu son warewa ke tafka adawa da juna.

Ya ce kaddamar da yarjejeniyar yankin cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA a takaice, cikin watan Yulin da ya gabata, ya nuna irin yadda kasashen nahiyar suka rungumi hadin gwiwa da juna, sabanin kariyar cinikayya.

Yarjejeniyar a cewar sharhin, ta share wata hanya ta kafa daya daga yankunan cinikayya maras shinge mafi girma a duniya, idan aka yi la'akari da yawan kasashen da ya kunsa, da yawan al'umma da suka kai biliyan 1.2, da kuma GDP da ya kai dala tiriliyan 2.5 dake karkashin wannan yarjejeniya.

Kaza lika ta hanyar kaddamar da yarjejeniyar AfCFTA, nahiyar ta dauki wani mataki na bunkasa hada hadar cinikayyarta, da raya masana'antunta, tare da samarwa yankin karin arziki.

A yanzu haka, matsayin hada hadar cinikayya tsakanin kasashen Afirka, bai wuce kaso 16 bisa dari na daukacin hada hadar da nahiyar ke yi ba, adadin da ya yi kasa matuka, idan aka kwatanta da na sauran nahiyoyin duniya, kamar Turai dake da kaso 69 bisa dari, da kuma nahiyar Asiya mai kaso 59 bisa dari, kamar dai yadda wasu alkaluma na MDD suka nuna.

Yarjejeniyar AfCFTA dai na fatan fadada hada hadar cinikayya tsakanin kasashen Afirka ta hanyar kawar da nau'o'in harajin hajoji, da ma 'yantar da hada hadar samar da hidimomi.

Har ila yau, baya ga cinikayya, AfCFTA na nuni ga amincewar da kasashen nahiyar suka yi cewa, gudanar da harkoki cikin hadin gwiwa, su ne kashin bayan warware batutuwa da suka jibanci kasa da kasa.

Baya ga yarjejeniyar AfCFTA, kasashen Afirka na kuma shiga a dama da su, a sauran al'amuran kasa da kasa, karkashin dandali daban daban, ciki hadda na Rasha da Afirka, da dandali na biyu na shawarar "ziri daya da hanya daya", na hadin gwiwar kasa da kasa da dai sauransu, wanda duka ke nuni ga amincewar nahiyar ga cudanyar sassa daban daban.

Ana dai hasashen cewa, nahiyar Afirka na sahun gaba wajen samun bunkasuwa a duniya cikin shekaru masu zuwa. Kaza lika ci gabanta a bangaren dunkulewar tattalin arziki, da rungumar salon cudanyar sassa daban daban, na iya bude mata damammaki na raya tattalin arziki, da ingiza manufofinta na samun dawwamammen ci gaba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China