Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurkawa na fakewa da hujjar kare 'yancin kai da tsaro wajen aiwatar da manufar keta hakkin sauran kasashe
2020-08-17 20:24:37        cri
Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana amfani da manhajar TikTok a kasar Amurka. Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Litinin cewa, yadda kasar Amurka ke cin zarafin kasar Sin ya nuna karyar da ta yi game da yin takara cikin adalci, ya kuma keta ka'idar cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma, ba kawai dokar za ta haddasa asara ga sauran kasashen duniya ba, har ma za ta kawo barazana ga kasar Amurka ita kanta.

Haka kuma, Zhao Lijian ya ce, wasu 'yan siyasan kasar Amurka suna daukar batun "kare tsaron kasa" a matsayin hujjar matsawa kamfanonin da ba na kasar Amurka ba lamba a ko da yaushe. Gwamnatin kasar Amurka ta ce, kamfanin ByteDance na Sin da ya kirkiri manhajar TikTok, da sauran wasu kamfanoni suna kalubalantar tsaron kasar Amurka, amma, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta CIA ba ta gano shaidun da suka nuna cewa, kasar Sin ta saci bayanan TikTok, ko kuma yin amfani da manhajar TikTok wajen satar bayanai daga wayoyin salulan jama'a ba. Bugu da kari, wasu kwararrun kasar Amurka sun nuna cewa, yadda kasar Amurka ta hana amfani da manhajar TikTok saboda na kasar Sin ne, bai shafi batun kare tsaron kasa ko kadan ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China