Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fara samun farfadowa a fannin bakatun sufurin jiragen sama
2020-08-11 13:46:07        cri
Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen saman kasar Sin CAAC ta ce, ana samun matukar farfadowar fannin sufurin jiragen sama a kasar tun daga watan Yuni, inda ake cigaba da samun karuwar bukatun harkar sufurin jiragen saman.

Alkaluman da hukumar ta CAAC ta fitar ya yi nuni da cewa, a watan Yuni, an gudanar da zirga-zirgar jiragen sama kimanin 325,000 a cikin kasar Sin, ke nan an gudanar zirga-zirgar kimanin 10,820 a kowace rana, adadin ya karu da kashi 14.1 bisa 100 daga watan Mayu.

A jimlace, an samu zirga zirgar fasinjoji ta jiragen sama wanda ya zarce miliyan 30.73 a watan Yuni, adadin da ya karu da kashi 10.2 bisa 100 idan an kwatanta da na watan Mayu.

A watan Yuli kuma, an gudanar da harkokin sufurin jiragen saman kimanin 370,000 a cikin kasar, wato kimanin 11,941 a kowace rana.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China