Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ingiza aikin gina manyan ababen more rayuwa na zamani a fannin zirga-ziraga
2020-08-07 13:36:40        cri
Hukumar zirga-zirga ta kasar Sin ta bada wata shawara a jiya Alhamis kan ingiza aikin gina manyan ababen more rayuwa na zamani a fannin zirga-zirga, inda ta nuna cewa, ya kamata a sa kaimi wajen yin amfani da fasaha mai inganci wajen gina manyan ababen more rayuwa a fannin zirga-zirga.

Ana sa ran cewa, Sin ta za ta samu gagarumin ci gaba a wannan fanni kafin shekarar 2035, inda za a iya kyautata karfin kirkire-kirkire a fannnin kimiya da fasaha, da kuma karfin amfani da wadannan kimiya da fasahohi ta yadda za su kai matsayin koli a duniya.

Ban da wannan kuma, shawarar ta ce, za a sa kaimi ga amfani da fasahar 5G da tsarin jagorancin zirga-zirga na Beidou da kuma tauraron Bil Adama masu dauke da na'urar gano abu a nesa da dai sauransu. Har ma da kara karfin yin amfani da tsarin Beidou ta fuskar zirga-zirga, da kuma kafa tsarin taswirar dogaro da Beidou, har ma da kara kwarin gwiwar al'umma wajen zuba jari ga manyan ababen more rayuwa masu amfani da kimiya da fasaha. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China