2020-02-25 19:32:15 cri |
Rahoton na bayyana cewa, a makon jiya, hanyoyin zirga-zirga a biranen Beijing, da Shanghai da Guangzhou na farfadowa. Ban da wannan kuma, a kwanan baya, a wasu cibiyoyin biranen Beijing, da Shanghai da Guangzhou, da Shenzhen, da na Hangzhou, har ta kai an samu cunkoso a hanyoyi da safe da kuma yammaci, lokacin da ake tafiya zuwa wurin aiki da kuma dawowa gida.
Mashahanta na nuna cewa, yawan zirga-zirga, zai yi nuni game da halin zirga-zirgar mutane, da kuma jigilar kayayyaki, matakin da ke share fagen budewar masana'antu yadda ya kamata sakamakon komawar ma'aikata bakin aiki. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China