Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeria za ta bude masallatai ga jama'a
2020-08-04 10:56:23        cri
Shugaban Aljeria, Abdelmadjid Tebboune, ya sanar a jiya cewa, kasarsa na duba yuwuwar sake bude masallatai ga jama'a.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya ruwaito shugaban na bayyana haka ne yayin taron majalisar tsaro da ya samu halartar manyan jami'an soji da sauran jam'an tsaro, tare kuma da ministoci, domin nazartar yanayin annobar COVID-19 a kasar.

Shugaba Tebboune ya umarci Firaminista Abdelaziz Djerad, ya shirya bude masallatan sannu a hankali.

Ya kara da cewa, da farko, shirin zai bude manyan masallatai 1,000, wanda zai bada damar bayar da tazara tsakanin mutane, sannan dole ne kowa ya sanya makarin baki da hanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China