Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nada ministan harkokin wajen Algeria a matsayin firaministan kasar na rikon kwarya
2019-12-20 09:25:04        cri
Zababben shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune a jiya Alhamis ya nada ministan harkokin wajen kasar, Sabri Boukadoum, don maye gurbin firaministan kasar Noureddine Bedoui, wanda ya mika takardar yin murabus.

Murabus din Bedoui ya zo ne 'yan sa'oi kadan bayan rantsar da Tebboune a matsayin sabon shugaban kasar Algeria.

Bayan nada Boukadoum a matsayin firaministan kasar na rikon kwarya, shugaba Tebboune ya maye gurbin ministan cikin gidan kasar Salaheddine Dahmoune, inda ya nada ministan ma'aikatar samar da gidaje, Kamel Beldjoud.

Tebboune ya bukaci majalisar ministocin kasar su cigaba da zama akan kujerarsu na rikon kwarya har zuwa lokacin da za'a kafa sabuwar majalisar ministocin kasar.

Tun da farko a ranar Alhamis ne, Tebboune ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar ta shiyyar arewacin Afrika na takwas.

Zaben Tebboune a matsayin shugaban kasar Algeriya ya zo ne watanni 10 bayan da aka fara zanga zanga a kasar don yin matsin lamba ga shugaba Abdelaziz Bouteflika da ya sauka daga mulki a watan Afrilu.

Masu zanga zangar suna neman a samu gagaruman sauye sauye, kana a kafa tsarin dokokin kasar.

Tebboune ya sha alwashin fara tattaunawa da dukkan bangarorin dake da ruwa da tsaki a zanga zangar, inda ya yi alkawarin kawo karshen tsohon salon shugabanci da ake amfani da shi a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China