2020-07-07 13:58:58 cri |
Dr Tom Jefferson, ya ce akwai wasu shaidu dake nuni da cewa, kwayoyin cutar sun kasance a wasu yankuna na duniya kafin bullar su a nahiyar Asiya.
Ko da a makon jiya ma, wani kwararren masanin kwayoyin cututtuka na kasar Sifaniya, ya bayyana gano birbishin kwayoyin cutar, a wasu samfuran ruwa da aka gwada cikin watan Maris na shekarar bara, kimanin watanni 9 kafin bayyanar cutar a kasar Sin.
Kaza lika wasu masana kimiyya na kasar Italiya, sun gano kwayoyin cutar cikin wani ruwan dagwalo a biranen Milan da Turin, tun a tsakiyar watan Disamba, makwanni da dama kafin gano masu dauke da cutar a karon farko. Har ila yau, wasu kwararrun sun gano birbishin kwayoyin cutar a kasar Brazil tun cikin watan Nuwambar bara.
Cikin wani bayani da aka wallafa a jaridar Telegraph, Dr Jefferson tare da daraktan cibiyar bincike ta CEBM farfesa Carl Henegehan, sun yi kira da a zurfafa bincike game da cutar ta COVID-19.
Dr Jefferson ya ce, tuni suka fara fadada nazari, tare da duba yanayi na muhalli, da muhallin rayuwar nau'oin wannan kwayar cuta, wadda kawo yanzu ba a da cikakkiyar masaniya game da ita. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China