
Da karfe 1 saura mintuna 19 na tsakar ranar yau Alhamis ne aka cimma nasarar harbar roka samfurin Changzheng-5, dake dauke da na'urar binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-1 da kasar Sin ta kera, kuma irin ta ta farko zuwa sararin samaniya, daga filin harbar taurarin dan Adam na Wenchang dake tsibirin Hainan na kasar Sin. (Zainab)