Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasinjoji 21 sun bace yayin da aka ceto wasu biyu a kifewar kwale-kwale a Najeriya
2020-07-06 11:40:26        cri

'Yan sanda sun sanar da cewa, mutane 21 ne aka tabbatar sun salwanta a ranar Lahadi bayan da wani kwale-kwale ya kife a kogin Benue wanda shi ne kogi mafi girma a shiyyar tsakiyar Najeriya.

Kakakin hukumar 'yan sandan jahar Benue, Catherine Anene, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami'an 'yan sandan masu tsaron teku sun yi nasarar ceto mutane biyu da ransu.

Jimillar fasinjoji 23 ne a cikin kwale-kwalen wanda ya nitse yayin da ya kai tsakiyar tekun a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Makurdi, babban birnin jahar.

Anene ta kara da cewa, an gano fasinjojin mabiya wata majami'a ne dake shirin halartar taron ibada a lokacin da hadarin ya faru.

Wannan hadari ya faru ne kwanaki biyu da faruwar makamancinsa, inda wasu mutanen 21 ciki har da matukin jirgin ruwan suka nitse a tekun jahar Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya. Shida daga cikin mutanen an tabbatar da mutuwarsu yayin da aka ceto mutane 14 da ransu, sai kuma fasinja guda wanda har yanzu ba'a same shi ba tun bayan faruwar hadarin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China