Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwajin da aka yiwa gwamnan jahar Ebonyi ya nuna ya kamu da COVID-19
2020-07-05 21:09:09        cri
Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.

Sannan wasu daga cikin makusantan gwamnan su ma gwajin da aka yi musu ya nuna suna dauke da cutar, kamar yadda Francis Nwaze, mataimaki na musamman ga gwamnan a fannin yada labarai ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Lahadi.

Sai dai Nwaze yace, kawo yanzu gwamnan bai nuna wasu alamun kamuwa da cutar ba, amma duk da haka ya killace kansa bisa ka'idar hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC.

Idan aka hada da Umahi, a jimlace an samu gwamnoni uku ke nan da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 cikin makonnin da suka gabata da suka hada da gwamnonin Ondo da Delta wadanda aka ayyana tun da farko sun kamu da cutar.

A ranar Asabar din da ta gabata, ana samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 kimanin 603 a Najeriya, yayin da jimillar wadanda suka harbu da cutar a kasar ya kai 28,167.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China