Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu dauke da COVID-19 a Ghana ya wuce 20,000
2020-07-06 11:35:20        cri

Kasar Ghana ta tabbatar da kamuwar karin mutane 697 da cutar COVID-19 a ranar Lahadi, hakan shi ya kara adadin mutanen da suka harbu da cutar a kasar zuwa 20,085, wannan shi ne alkaluma na baya bayan nan da hukumar lafiyar Ghana ta ayyana.

Hukumar ta bayyana cewa, mutane 14, 870 sun warke daga cutar, bayan da aka samu karin mutane 540 da suka warke.

Ghana ta yi hasarar karin mutane biyar, wanda ya kawo adadin mutanen da COVID-19 ta kashe a kasar zuwa 122.

Kasar ta yammacin Afrika ta yi alkawarin daukar kwararan matakan yaki da cutar COVID-19, yayin da kasar ta kammala tattara rejistar masu zabe a ranar 30 ga watan Yuni gabanin babban zaben kasar dake tafe a watan Disamba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China