Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Ghana sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashensu
2020-07-05 15:59:41        cri

A yau Lahadi shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, sun gabatar wa juna sakon taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A sakon nasa, Xi ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu shekaru 60 da suka gabata, kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana ta kara karfi, kana ta haifar da kyawawan sakamako.

Shugaba Xi ya kara da cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19,  Sin da kasashen Afrika, ciki har da Ghana, suna hadin gwiwa da juna wajen yaki da annobar, wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar 'yan uwantaka dake tsakanin Sin da kasashen Afrika inda suke fuskantar wahalhalun da kalubalolin tare.

Da yake jaddada muhimmancin dake tattare da bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, Xi ya ce, a shirye yake yayi aiki tare da Akufo-Addo wajen yin amfani da bikin cika shekaru 60 da kafuwar alakar kasashen a matsayin wata muhimmiyar damar daga matsayin abokantakar dake tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa a fannoni da dama karkashin hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, domin amfanawa kasashen biyu da al'ummomin kasashen, da kuma bayar da gudunmawa wajen kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin al'ummomin Sin da Afrika don samar da makoma mai inganci ga jama'ar sassan biyu.

A nasa bangaren, Akufo-Addo yace, tsoffin shugabannin kasashen biyu, da suka hada da marigayi tsohon shugaban Ghana Kwame Nkrumah, da tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong, da tsohon firaministan kasar Marigayi Zhou Enlai, sun yi hadin gwiwa da juna wajen kafa dangantakar dake tsakanin kasashen Ghana da Sin.

Ya kara da cewa, shugaba Xi ya nuna bajinta wajen bada jagoranci a yaki da annobar COVID-19, kuma a cewarsa kasar Sin ta samu martaba da kima a idanun kasa da kasa bisa irin taimako da tallafin da ta baiwa kasashen duniya, ciki har da kasar Ghana, domin yaki da cutar.

Ya kara da cewa, kasar Ghana, ta nuna cikakken goyon baya ga kokarin yaki da COVID-19 ta hanyar hadin gwiwa da yin aiki tare da kasa da kasa.

A wannan rana kuma, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Mr. Wang Yi tare da takwararsa ta kasar Ghana Madam Shirly Ayorkor Botchway, sun kuma mika wa juna sako na taya murnar ranar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China