Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Amurka ke neman bata yanayin yankin Hong Kong aikin banza ne
2020-07-03 15:12:39        cri
Kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da daftarin dokar cin gashin kai na yankin Hong Kong na kasar Sin, inda ta kalubalanci cewa, za ta kakaba wa duk wanda ke bata yanayin cin gashin kai na yankin Hong Kong. Wannan matakin da kasar Amurka ta dauka tamkar kasance tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda ya keta dokokin kasa da kasa da babbar ka'idar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, ta kuma nuna burinta na nuna kiyayya ga kasar Sin da haddasa tashe-tashen hankula a yankin Hong Kong, amma dukkan kokarin da ta ke yi domin cimma wannan buri ayyukan banza ne.

Batun kare tsaron kasa, shi ne tushen kiyaye da raya ko wace kasa, ko wace kasa tana da ikon kafa dokar kare tsaronta. Yadda kasar Sin take kafa da kyautata dokar tsaron kasa dake shafar yankin musamman na Hong Kong ya dace da dokokin kasa da kasa da kasashen duniya suka saba bi. A yayin taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 44 da aka yi kwanan baya, kasar Cuba a madadin kasashe guda 53, sun yi maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, ana bin ka'idar adalci.

Cikin dokar kare tsaron kasa dake shafar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, an zayyana yadda za a hukunta laifin neman raba kasa, da laifin yunkurin juyin mulki, da laifin ta'addanci, da kuma laifin zama 'yan kanzagin wasu bangarorin kasashen waje. Tambayar da muke son yi wa kasar Amurka ita ce, cikin wadannan laifuffuka, wane ne bai keta dokar Amurka ba? Ko ta manta da hadarin harin ta'addancin da aka kai mata a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001? Kasar Amurka tana da dokokin tsaron kasa iri daban daban, me ya sa, ba ta son kasar Sin ta kafa dokar kare tsaron kasarta? Yadda Amurka ta nuna fuska biyu ya bata ran al'ummomin kasa da kasa kwarai da gaske!

Bayan da aka gabatar da dokar kare tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong, duk wani kokarin da masu neman raba kasar Sin za su yi, aikin banza ne, ya kamata 'yan siyasar kasar Amurka su daina tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong, domin suna bata lokacinsu ne. Abin da ya fi kyau yanzu, shi ne su mai da hankali kan yadda za su hana yaduwar annobar cutar COVID-19 a cikin kasarsu, da kuma ceton rayukan al'ummomin kasar yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China