Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude makon kasuwanci ta kafar intanet tsakanin Sin da Afirka
2020-06-30 13:24:20        cri
An kaddamar da makon kasuwanci ta kafar sadarwar intanet karo na farko tsakanin Sin da Afirka jiya Litinin, inda hukumomin gwamnati daga kasashen Afirka 10 suka halarci bikin kaddamar da makon ta kafar intanet.

A yayin bikin, kamfanonin kasar Sin sama da dubu daya za su gudanar da harkokin kasuwanci ta kafar bidiyo da kamfanonin Afirka kusan dubu 10, inda za su gudanar da ciniki a bangarori daban-daban, ciki har da gine-gine, da makamashin wutar lantarki, da abinci, da aikin gona, da kiwon lafiya da otel-otel da kayan gida da sauransu.

Haka kuma a yayin makon, bangarori daban-daban za su yi taro da shirya "dandalin tattaunawa kan kasuwanci ta kafar intanet tsakanin Sin da Afirka", da sauran wasu ayyukan tallata kasashen Kenya da Ghana da Morocco, da kuma gayyatar kwararru da masana don su yi bayani kan manufofi da tattalin arziki gami da bunkasuwar sana'o'i a kasashen na Afirka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China