Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya yi gargadi game da kudaden bai daya na shiyya
2020-06-24 14:23:28        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi takwarorinsa na kasashen yammacin Afrika da su yi hattara game da hadarin dake tattare da kudaden bai daya na shiyyar wato Eco a takaice.

Buhari ya yi wannan tsokaci ne a wannan mako a babban taron shugabannin kasashen Afrika da manjan jami'an hukumomin kudi na kasashen yammacin Afrika WAMZ ta kafar bidiyo game da batun sabon kudin bai daya na shiyyar.

Shugaban ya bayyana damuwa game da matakin da kasashen renon Faransa suka dauka na kafa kungiyar hadin gwiwar samar da sabon kudin bai daya na gamayyar kasashen yammacin Afrika UEMOA, domin maye gurbin kudin CFA Franc da sabon kudin na Eco a tsakanin kasashen.

Shugaba Buhari ya jaddada aniyar Najeriya game da kudin na bai daya, kana ya bukaci shugabannin kugiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin ECOWAS, da su yi la'akari da shawarwarin da aka cimma a taron kungiyar domin gudun kada gamayyar WAMZ ta dauki matakan da za su haifar da fadawa cikin hadari. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China