Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta fadada samar da kayayyakin gaggawa na kiwon lafiyar al'umma
2020-06-17 10:10:59        cri
Hukumar tsara manufofin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, ta ce za a fadada samar da kayayyakin gaggawa na kiwon lafiyar al'umma, ta hanyar inganta hidimomin kandagarki da jinyar marasa lafiya, da kara yawan kayan aiki da ake sarrafawa domin al'umma.

A cewar kakakin hukumar tsara manufofin ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin Meng Wei, tun a watan Afrilun da ya gabata, gwamnatin tsakiya ta kasar, ta amince da wani tsari na fadada samar da kayayyakin gaggawa na kiwon lafiyar al'umma, wanda manufarsa ita ce shawo kan matsaloli, da inganta sassan da ke da rauni, da ma karfafa dukkanin matakan shawo kan duk wani kalubale na lafiya da ka iya bijirowa ba tsammani.

Meng ya kara da cewa, Sin za ta fadada zuba jari a fannin gina cibiyoyin kandagarki da shawo kan cututtuka a matakai daban daban, da samar da managartan dakunan gwaje-gwajen halittu masu rai, inda ake sa ran ko wane yanki mai matsayin lardi, ya zama yana da a kalla dakin gwaji daya na P3 da ke iya gudanar da ayyuka masu nagarta.

Hakan a cewar jami'in na da nufin karfafa ayyukan sa ido, da samar da bayanan yiwuwar barkewar duk wata cuta cikin hanzari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China