Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi gargadi game da yiwuwar ambaliya a lokacin damina
2020-06-11 19:02:07        cri

Mataimakin ministan albarkatun ruwa na kasar Sin Ye Jianchun, ya yi gargadi game da tsanantar yanayi a lokacin damina, inda ya bukaci dukkan sassan da abin ya shafa, da su shiryawa yiwuwar manyan ambaliyar ruwa.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai, ya ce, a yayin da kasar Sin ta shiga lokaci na manyan ambaliyar ruwa, akwai koguna 148 da suka zarce mizanin gargadi na yin ambaliya.

A cewar ma'aikatar, a wannan shekarar, an yi ruwan sama masu karfin gaske sau 18. Kana daga ranar 2 ga watan Yuni zuwa wannan lokaci, akwai larduna 12 da suka samu ambaliya, abin da ya kai sama da milimita 400 na ruwa a yankin da ya kai sama da muraba'in kilomita 24,000.

Ye ya ce ma'aikatarsa ta bukaci kananan hukumomi, da su shirya matakan kare rayukan jama'a, koda wadanda ake da su, ba za su iya jure ambaliyar da za a iya samu ba.

Haka kuma, ma'aikatar tana aiki da sauran hukumomi, don inganta tsarin gargadi, don tabbatar da cewa, mutanen dake zaune a wurare mafiya hadari, sun samu gargadi a kan lokaci. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China