Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan na kasar Sin za ta kawo sabuwar dama ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2020-06-09 14:04:52        cri

Gwamnatin kasar Sin, ta gudanar da taron manema labaru a jiya, inda aka yi bayani game da shirin gina tashar yin cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan.

A gun taron manema labarun da aka gudanar game da shirin gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan, an shaida cewa, cutar COVID-19 ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya, bisa yanayin gaza raya duniya bisa tsarin bai daya, da ra'ayin bada kariya ga cinikayya, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon bayan ra'ayin bangarori daban daban, da kuma sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya.

Gina tashar yin cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan, muhimmin matakin bude kofa ne da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tsara, da sa kaimi ga aiwatar da shi. An jaddada cewa, ya kamata a inganta tashar zuwa wurin mafi bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a kasar Sin.

Don cimma wannan buri, ya kamata a tsara ka'idojin yin cinikayya na kasa da kasa masu inganci a tashar. An gudanar da manufofi a fannonin yin cinikayya, da zuba jari, da hada-hadar kudi a tsakanin kasa da kasa, da zirga-zirgar mutane, da yin jigila cikin 'yanci da sauki, da sadarwa mai inganci da sauransu a tashar. A karkashin hakan, an samar da 'yanci da sauki ga cinikin kaya ba tare da biyan haraji ba, da kuma soke yin bincike, da amincewa da gwamnatin lardin Hainan ke yi, muddin babu wasu ka'idoji ko dokokin da ya wajaba a yi aiki da su, don sa kaimi ga bunkasa kasuwanni a fannoni daban daban.

Kana ana yin kirkire-kirkire bisa tsarin kasar Sin na musamman don kara bude kofa ga kasashen waje. An ce, game da batun yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci da sauki, za kuma a kafa tsari da dokoki dake shafar dukkan fannoni a tashar, don sa kaimi ga samar da kayayyaki, da yin ciniki cikin 'yanci, da kuma magance hadari a fannoni daban daban.

Bisa shirin da aka yi, za a tsara takardar sassan da baki ba za su iya zuba jari a ciki ba a tashar a fannin hidimar kasashen waje, wannan ne karo na farko da aka tsara irin wannan takarda a wannan fanni a kasar Sin.

Ana iya ganin cewa, gina tashar yin cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ta tsibirin Hainan, ya shaida kokarin kasar Sin wajen kara bude kofa ga kasashen waje, da kuma canja tsarin bude kofarta, daga cinikin kaya zuwa fannin tsara ka'idoji da tsari.

A watan Oktoba na shekarar 2019, majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar da ka'idojin kyautata yanayin yin cinikayya, inda aka maida matakai da fasahohin kyautata yanayin yin cinikayya zuwa ka'idoji, ta yadda hakan zai tabbatar da yanayin yin cinikayya na kasar Sin bisa dokoki. A ranar 1 ga watan Janairun bana, an fara aiwatar da dokar zuba jari ta kamfanonin kasashen waje, inda aka gabatar da ka'idoji a fannonin kare ikon mallakar ilmi, da fasahohin kamfanonin jarin waje, da nuna matsayin daidaito ga jarin waje kafin masu su, su soma zuba jari, da kuma daidaita takardar sassan da baki ba za su iya zuba jari a ciki ba, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsarin bude kofa a fannin tsara ka'idoji da dokoki.

Kod a yake ana fuskantar kalubalen da cutar COVID-19 ke kawowa, amma a maimakon rufe kofa, kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje. Gina tashar da kasar Sin ke yi ya shaidawa duniya cewa, Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga yin cinikayya, da zuba jari cikin 'yanci da sauki, don sa kaimi ga bude kofa da hadin gwiwa a dukkan duniya baki daya.

Ana sa ran cewa, ta hanyar gina tashar, za a biya bukatun juna a tsakanin tashar da sauran tashoshin yin cinikayya cikin 'yanci dake dab da ita, da yin kokarin samun bunkasuwa tare, wanda hakan zai kara jawo hankali ga kasuwar kasar Sin, da kara samar da dama ga kamfanonin kasa da kasa, don sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China