Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitocin kasar Sin a Ghana: A shirye muke mu samar da gudummawarmu wajen dakile cutar COVID-19
2020-04-24 14:39:17        cri






Malam Shi Yongyong wanda ya fito daga asibitin maganin gargajiya na lardin Guangdong na kasar Sin shugaba ne na tawagar likitocin da kasar Sin ta tura zuwa kasar Ghana karo na tara, don samar da gudummawar jinya. A kwanakin baya, yayin da yake tattaunawa da wakiliyarmu ta wayar tarho, ya ce a yayin da ake tsaka da fama da cutar numfashi ta COVID-19, a shirye suke su samar da gudummawarsu ga kasashen Afirka idan bukatar hakan ta taso.

Malam Shi Yongyong mai shekaru 41 da haihuwa, ya taba sa hannu a aikin yaki da cutar Sars a shekarar 2003, a lokacin shekaru biyu kadai ya yi da kama aikin likita. A wannan karo, bayan da ya shafe tsawon rabin shekara yana samun horo tare da sauran 'yan tawagarsa 10 a birnin Guangzhou, sun tashi zuwa Ghana a ranar 28 ga watan Disamban bara. Barkewar cutar COVID-19 a kasar Sin a farkon watan Janairun bana ma ta jawo hankalinsu, kuma nan da nan suka fara daukar matakai. Ya ce, "Tuni a ranar 22 ga watan Janairu, muka gabatar da shawara ga Sinawa mazauna kasar Ghana da ma ma'aikatan kamfanonin kasar Sin da ke wurin, inda muka shawarce su da su rage zirga-zirga. Wadanda suka zo daga gida kasar Sin kuma, sai mu shawarce su da su killace kansu a gida."

Bayan da aka fara gano bullar cutar a kasar Ghana a ranar 12 ga watan Maris da ya wuce, gwamnatin kasar ta dauki jerin matakai na kare yaduwar cutar, ciki har da rufe iyakar kasa da makarantu da hana gangamin jama'a da sauransu. A sa'i daya kuma, ana kokarin bibiyar wadanda suka yi mu'amala da masu cutar, tare da yi wa wadanda ake shakkar sun harbu da cutar gwajin. Ya zuwa ranar 20 ga wata, hukumomin lafiya na kasar ta Ghana sun yi wa samfura sama da dubu 68 gwaji, kuma gaba daya ta tabbatar da mutane 1042 da suka kamu da cutar, lamarin da ya sa kasar ta zama daya daga cikin kasashe uku da suka fi gano masu harbuwa da cutar a kudu da Sahara

A yayin da ake tsaka da shawo kan cutar, ayarin likitocin kasar Sin da ke Ghana na kokarin taimakawa gwamnatin kasar da ma asibitin da suke aiki wajen kandagarkin cutar, inda suka gabatar da fasahohi da dabaru na kasar Sin ga kwararrun masanan yaki da cutar na kasar Ghana. A sa'i daya kuma,sun kuma fitar da kananan littattafai na wayar da kan al'umma game da matakan kare kai daga cutar. Bisa kokarin da suka yi, an samu jerin sauye-sauye a asibiti. Malam Shi Yongyong ya ce, "A baya, abokan aikinmu 'yan kasar Ghana ba su saba da sa marufin baki da hanci ba, amma bayan da muka yi shawarwari da su, sannu a hankali sun gyaru. Yanzu haka dukkanin likitoci da nas nas da ke aiki a asibitinmu suna sanya marufin baki da hanci. Ban da haka, duk wanda ya shigo asibiti don a duba lafiyarsa ma za a ba shi marufin baki da hanci ya sanya. A bakin kofar asibitin kuma, an kafa na'urar wanke hannu, kuma ya zama dole ga duk wanda ya shigo asibiti ya wanke hannu tukuna, sa'an nan a auna zafin jikinsa tare da duba sauran alamu masu alaka da cutar COVID-19."

Duk da cewa gwamnatin Ghana ta dauki managartan matakai a farkon barkewar cutar, har ma ta fara gina wani asibiti na killace masu cututtuka masu yaduwa, amma har yanzu yawan masu kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa. Malam Shi Yongyong ya ce, asibitin da ayarin likitocin kasar Sin ke aiki a Ghana, ba asibiti ne da aka kebe musamman domin jinyar masu cutar COVID-19 ba, amma likitocin kasar Sin suna da niyya da kuma kwarewa wajen taimakawa wadanda ke bukatar taimakonsu. A cewarsa, a shirye suke su samar da taimakonsu idan gwamnatin kasar ta bukace su. Ya ce, "Mun zo nan Ghana ne don bada taimakonmu, kuma dukkan likitocinmu sun bayyana cewa, a shirye suke su ba da taimakonsu idan bukatar hakan ta taso."

A farkon barkewar cutar, gwamnatin kasar Ghana ta samar da gudummawar marufin baki da hanci samfurin N95 ga birnin Wuhan na kasar Sin. Sai kuma a lokacin da kasashen Afirka suke fuskantar wahala, nan da nan gwamnatin kasar Sin da ma kamfanoni masu zaman kansu na kasar suka ba da taimakonsu, inda suka tura kayayyakin kandagarkin cutar zuwa kasar. A ranar 16 ga wata, tawagogin kwararrun likitoci biyu da gwamnatin kasar Sin ta tura suka isa kasashen Habasha da Burkina Faso, don su hada kai da hukumomin lafiya na kasashen wajen shawo kan cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China