Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Lesotho ya yi murabus
2020-05-20 11:01:56        cri

Firaministan Lesotho, Thomas Thabane, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa a jiya Talata.

cikin jawabin da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar talabijin ta kasar daga birnin Maseru, Thomas Thabane ya ce , ya sanar da cewa, duk da cewa aikin da aka dora masa bai kare ba, amma kuma lokacin murabus daga aikin ya yi, yana mai cewa lokacin daukar hutu daga aiki ya zo.

Murabus din nasa na zuwa ne, bayan a makon da ya gabata, majalisar dokokin kasar ta rusa gwamnatin hadaka da yake jagoranta, lamarin da ya bada dama ga kafa sabuwar gwamnati da sabon Firaminista.

An shafe watanni, Firaministan mai shekaru 80 na fuskantar matsi don ya sauka daga mukaminsa, bayan an zarge shi da hannu cikin kisan da aka yi wa tsohuwar matarsa Lipolelo Thabane, a shekarar 2017. Har ila yau, ana zargin matarsa ta yanzu da hannu a kisan.

Za a rantsar da Ministan kudin kasar, Moeketsi Majaoro, a matsayin wanda zai maye gurbin Thomas Thabane, wanda ya yi alkawarin goyon bayan sabon firaminstan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Wang Yong ya kai ziyarar aiki a Lesotho 2019-12-15 16:35:54

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China