Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban firamare da sakandare miliyan 180 sun yi karatu ta yanar gizo a lokacin annoba
2020-05-15 13:25:43        cri
Shugaban sashen ba da ilmi na tushe, na ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin Lu Yugang, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, a lokacin barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, kasar ta ba da ilmi ga daliban firamare, da na sakandare miliyan 180 ta yanar gizo, domin tabbatar da ci gaban karatunsu a lokacin annobar, lamarin da ya inganta musayar ayyukan ba da ilmi.

Shi ma shugaban kula da harkokin ba da ilmi a jami'a na ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin Wu Yan ya ce, a lokacin barkewar cutar numfashi ta COVID-19 tsakanin kasa da kasa, kasar Sin ta yi musaya da gamayyar kasa da kasa, kan sakamako da fasahohin ba da ilmi ta yanar gizo, har ma ta kafa dandalin ba da ilmi ta yanar gizo na harshen Turanci, ta kuma saka darussa 302 na harshen Turanci cikin dandalin, wadanda suka shafi fannoni guda takwas, da suka hada da likitanci, yin kandagarki kan cutar COVID-19, raya muhallin halittu, da aikin injiniya, da aikin gona, da tattalin arziki da dai sauransu, domin ba da taimako ga daliban jami'a na kasa da kasa.

Dangane da wannan batu, shugabar sashen manufofin kimiyya da fasaha na hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al'ada ta UNESCO Peggy Oti-Boateng ta bayyana cewa, ba kawai dandalin ba da ilmin da kasar Sin ta kafa yana ba da gudummawa ne ga kasar Sin ita kadai ba, har ma, yana ba da gudummawa ga kasashen duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China